Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na bbc bangaren turanci ya habarta cewa, an kame wani mutum dan shekaru talatin da biyar da yake aikewa da wasiku yana yi musulmi barazana a kasar Birtaniya da yake zaune a raewacin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan mutum yana daga cikin mutanen da ske nuna tsananin kiyayya ga musulmi a kasar ta Birtaniya.
A cikin wasikun da yake aikewa, yana yin barazana ga musulmi, tare da tsorata su, da kuma yi musu barazana.
Tun bayan kai hare-haren ta’addancin da aka yi a lokutan bayan-bayan nan akasar Birtaniya, kyamar musulmi na ci gaba da karuwa a sassa daban-daban na kasar.